Bbchausa - bbchausa.com

General Information:

Latest News:

Madonna ta fi dukkan taurari samun kudi 27 Aug 2013 | 09:10 pm

Shahararriyar mawakiyar nan Madonna ta fi kowanne tauraro da tauraruwa samun kudi a duniya, inda ta wuce Oprah Winfrey da Steven Spielberg, a cewar mujallar Forbes.

Wani gini ya rufta da mutane uku a Abuja 27 Aug 2013 | 08:32 pm

A Najeriya mutane akalla uku ne aka ba da rahoton sun mutu, yayin da wasu suka jikkata bayan wani sashe na wani sabon gini da suke aiki a kai ya rufta, a Unguwar Maitama dake Abuja.

'Fargabar yaduwar cututtuka a Najeriya' 27 Aug 2013 | 07:11 pm

Hukumar kula da lafiya a matakin farko a Najeriya ta nuna damuwa game da yiwuwar yaduwar wasu cututtuka masu hallaka kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Malawi ta kai karar Keshi wajen FIFA 27 Aug 2013 | 07:02 pm

Hukumar kwallon kafa ta Malawi ta gabatar da korafi a gaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, game da kalaman mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi.

Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da sojoji 27 Aug 2013 | 06:43 pm

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarunta na tabbatar da zaman lafiya hudu sun bace a yankin Darfur na Sudan bayan da ambaliyar ruwa ta tafi dasu.

Dakaru na jiran umurnin Obama a kan Syria 27 Aug 2013 | 05:26 pm

Sakataren tsaron Amurka, Chuck Hagel, ya gayawa BBC cewa dakarun kasar a shirye suke su kai hari a kan Syria, idan har Shugaba Obama ya basu umurni.

Hotuna harin makamai masu guba a Syria 27 Aug 2013 | 05:07 pm

Yadda makamai masu guba suka janyo mutuwar daruruwan mutane a kasar Syria.

Iyalai daga Najeriya na gudun hijira a Chadi 27 Aug 2013 | 02:51 pm

Jama'a da dama ne ke kwarara cikin kasar Chadi daga Najeriya, domin gujewa farmakin da dakarun Najeriyar ke kaiwa 'ya 'yan kungiyar nan da ake kira da Boko Haram.

Rasha da China sun ce a yi taka tsan-tsan 27 Aug 2013 | 02:43 pm

Rasha da China sun kara yin gargadi game da yinkurin amfani da matakin soji a kan Syria, inda suka ce kasashen yammacin duniya sun yi gaggawar yanke hukunci.

Shirin samar da abinci a Indiya 27 Aug 2013 | 12:25 pm

Wani shirin samar da abinci a farashi mai sauki na fiye da dala biliyan goma sha takwas ga talakawan Kasar Indiya ya sami hayewa a majalisar wakilan Kasar.

Recently parsed news:

Recent searches: